Hausawa Mutane Kirki Ne, Fulani Sune Matsalar Najeriya – Inji Nnamdi Kanu

Shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra, IPOB, Mazi Nnamdi Kanu ya ce ‘yan kabilar Igbo ba su da wani abin da zai hana su mu’amala da Hausawa a Najeriya saboda su (Hausawan) mutane kirki ne kuma sun iya zama da mutane.

Ya kuma ce na Fulani ne ke ba wa ‘yan kabilar Ibo da sauran kabilun Najeriya matsala, ya kara da cewa yanzu suna son shigo da Hausa cikin matsalolin da ake zargin sun haifar a Najeriya, tare da kalmar, Hausa-Fulani.

A karshe Kanu Shugaban ya yi kira ga Hausawa da kar su bari Fulani su yaudaresu da kalmar Hausa-Fulanai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here