FARASHIN BREDI ZAI YI SAMA A JIHAR KATSINA

A zantawar da wata kafar yada labaru ta yi da masu sana’ar sayar da bredi a cikin garin Katsina ta yi sun tabbatar da cewar yanzu haka dukkanin shire-shire sun kammala wajen kara farashin bredin.

Yanzu haka dai masu sana’ar sayar da bredi a jihar sun Sokoto sun fada yajin aiki tsawon kwanaki uku a sanadiyar tsangwama da su ka samu daga jama’a bayan da su ka yi yunkurin kara farashin bredin

Hujjar da daya daga cikin ma su sana’ar sayar da bredi a jihar Katsina ya bayar ita ce karin farashin ba ya rasa nasaba da Karin farashin sukari da flawa wanda su ka ce sun kusa linka kudaden su akan farashin su na watannin baya

Hasashe dai na nuna cewar daukar mataki ga ma su sana’ar sayar da bredi na Jihar Katsina makamancin na Sokoto na iya kaiwa ga jefa “yan kungiyar bredin shiga yajin aiki wanda kuma hakan zai iya bayar da dama ga abokanan sana’ar su daga wa su jihohin su rika kawo bredin na su garin Katsina da kuma zai kai ga karya wa su daga cikin ma su sana’ar a garin Katsina.

Yanzu dai abin jira a gani shine yanayin farashin da za’a karawa bredin bayan sauran kayan masarufi da tuni sun riga sun ta shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here