Hauhawar farashi ya sake jefa ƴan Najeriya miliyan bakwai cikin talauci – Bankin Duniya
BBC Hausa
Ƙwararru a fannin tattalin arziƙi a Najeriya sun fara bayyana ra’ayoyinsu kan wani rahoton Bankin Duniya da ya yi gargaɗi game da ƙaruwar hauhawar farashi a ƙasar.
A cewarsa cikin watan Afrilun da ya wuce an samu hauhawar farashi mafi yawan da ba a taɓa gani ba a cikin shekara huɗu.
Haka kuma rahoton ya ce hauhawar farashin kaya ya sake jefa ‘yan Najeriya kimanin miliyan bakwai cikin matsanancin talauci a bara kaɗai.
Mukhtari Adamu Bawa ya ga ƙunshin rahoton ga kuma ƙarin bayaninsa.