Harkar Yima Yara Fyade tana Kara Ta’azzara a Katsina.

Muhammad Aminu Kabir

Lallai rashin zartar da Hukunci mai tsanani ga masu aika laifuka shi yake sanyawa ake samun yawaitar aukuwar laifukan.

Rundunar Yansandan Jihar Katsina ta Bayyana cewa tsakanin 9th – 14th January, 2021, tayi Nasarar chafko Mutane Tara da ake zargi da yima Yara kanan Fyade a Mabanbantan wurare anan Jihar Katsina, wannan yana kunshe ne cikin koke Shidda da Alumma suka shigar zuwa ga Hukumar ta Yansanda kamar yadda zaa zayyana su anan kasa.

Fyade: a ranar 14/01/2021 wata baiwar Allah mai suna Magajiya Ashababu, daga Unguwar Yammawa anan Katsina, ta shigar da kara a Offishin Yansanda dake CPS Central Police Station, Katsina, cewa wani Mutum mai suna Lawal Sani, Dan Kimanin Shekaru 62 dake zaune a Unguwar Sokoto Rima Katsina, ya yaudari diyarta yar Kimanin Shekaru 13 Inda yayi lalata da ita da karfin tsiya, Rundunar tana cigaba da Bincike akan Lamarin.

Haka nan a ranar 09/01/2021, wani Mai Suna Ibrahim Sale, daga Karamar Hukumar Charanchi jihar Katsina, yakai koke a Offishin Yansanda dake Rimi Divisional Police Headquarters, cewa wani Ibrahim Tukur, Dan Kimanin Shekaru 38yrs dake kauyen Kadandani a Karamar Hukumar ta Rimi lokaci daban daban ya yaudari diyar shi yar Kimanin Shekaru 12 yayi lalata da ita harma yayi mata ciki ta haihu, Yansanda suna cigaba da Bincike akan Lamarin.

A wani abu kuma da ba saban ba: a ranar 11/01/2021 wasu Mata sun kai koke kamar haka: (1) Rafa’atu Aminu (2) Aisha Abdullahi (3) Binta Aminu da (4) Maryam Aminu dukkanin su daga Unguwar Kofar Sauri dake nan cikin Birnin Katsina, Inda suka kawo koken (1) Auwal Hamza, Dan Kimanin Shekaru 20 (2) Suleman Abubakar, Dan Kimanin Shekaru 17 da (3) Abubakar Buhari ‘Dan Kimanin Shekaru 19 dukkan su daga Unguwar Kofar Sauri Katsina, cewa sun hada kai tareda Yaudarar Yaransu (1) Yusuf Isma’ila, ‘Dan Kimanin Shekaru 10 (2) Mohammed Aminu, Dan Kimanin Shekaru 8 (3) Umar Aminu, Dan Kimanin Shekaru 8 da (4) Abdullahi Aminu, ‘Dan Kimanin Shekaru 9 dukkan su daga Unguwar Kofar Sauri, zuwa wani kango Inda suka yi luwadi dasu Subhanallahi, ana cigaba da Bincike akan Lamarin.

Kazalika a ranar 10/01/2021, wani Mutum mai suna Sada Abdullahi, daga Kauyen Guza, cikin Karamar Hukumar Rimi ta Jihar Katsina yakai koke a Offishin Yansanda dake Rimi Divisional Police Headquarters akan cewa wani Isyaku Sani, ‘Dan Kimanin Shekaru 25 da suke zaune Gari daya an kama shi a cikin Wani kango a kauyen na Guza Inda yake saduwa da yaron nashi ta baya, Yaron mai Suna Umar Sada, ‘Dan Kimanin Shekaru 6 shima ana cigaba da Bincike.

Haka nan kuma a ranar 14/01/2021 wani mai Suna Mu’azu Sani, daga Unguwar Makudawa nan cikin Birnin Katsina, yakai kara a Offishin Yansanda dake CPS Katsina akan wani Sani Kabir, ‘Dan Kimanin Shekaru 18 da suke Unguwa daya ya yaudari diyar shi yar Kimanin Shekaru Goma Sha Daya 11zuwa wani Gida Inda da karfi ya cire mata wando ya kuma yi lalata da ita, ana cigaba da Bincike akan Lamarin.

A ranar 11/01/2021 Malama Jamila Salisu, dake Tsohuwar Unguwar B.C.G a Garin Funtua takai kara a Offishin Yansanda na CPS dake Funtua akan wani Sa’idu Yahaya, ‘Dan Kimanin Shekaru 21 da suke Unguwa daya wanda ya yaudari diyar yar Kimanin Shekaru 5 zuwa bayan Gida Inda yayi lalata da ita, ana cigaba da Bincike akan Lamarin.

Innalillahi wa Inna Ilaihir Raji’un, wannan Lamarin yayi Muni da yawa kullum Alamarin sai kara lalacewa take abun har takai ga Kananan Yara ma sunayi subhanallahi Allah kajikan mu ba dan halin mu ba Amin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here