HARIN ‘YAN BINDIGA A GOBIRAWA TA BATSARI, YADDA ABIN YA KASANCE.

A ranar lahadi ne wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne masu satar shanu da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, suka afka kauyen Gobirawa a daidai lokacin da suka kammala sallar isha’i (7:45pm), da isar su kauyen, kawai suka hau mutane da duka da sanduna wasu kuma suna harbi saman iska, amma dai ba’a samu asarar rai ba ko wani mummunan rauni, mazauna kauyen sun bayyana mana cewa sun sace wayoyin hannu (smart phone/touching) da dama sannan sun sace kudin wani mai sai da katin Waya #44000 da katin Waya na #7000, sai kuma #30000 na wani bawan Allah, daga nan kuma sun fada shagon wani mai shayi inda suka sace burodi, kwai, taliya, madara, da sauransu, haka kuma sun balle shagunan tireda inda nan ma suka saci abin da ran su yayi masu dadi.

Sun kwashe sama da awa daya suna cin Karen su ba babbaka duk da cewa tsakanin kauyen da inda sojoji suke zaune bai wuce nisan 4km ba, amma daga bisani jamian tsaro sun kawo masu dauki, saidai kuma sun riga sun sulale. Wata majiya ta bayyana mana cewa sun sace wasu shanu a garin amma daga bisani sun sako shanu.

A wani labarin da ya shigo mana yanzu, na cewa kauyen ya fashe kowa ya nemi mafaka domin tsira da ransa, domin wasu mazauna garin sun bayyana mana cewa sun ga babura bila adadin sun tunkaro kauyen nasu, sai dai sunce sun ci burki gidajen wasu fulani dake kusa dasu inda suka ce jami’an tsaro sunkai samame yau har sun kona gidajen su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here