HARIN ‘YAN BINDIGA A GARIN ‘YAN DAKA

Harin ƴan bindiga a garin yan daka ta karamar hukunar batsari, Barayin sun dau lokaci suna cin karensu babu babbaka

HARIN ‘YAN BINDIGA A YANDAKA.
…sun dauki lokaci suna ta asa
…Ana zargin harda yi ma Mata fyade
Da misalin karfe 12:00am na daren ranar alhamis 7/10/2020 wasu gungun ‘yan bindiga suka mamaye kauyen ‘Yandaka dake yankin Karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
‘Yan bindiga dauke da bindigogin bature sun bi gida gida sun sace abin da yayi saura na dabbobin mutanen, sannan sun balle shaguna sun sace kayan dake ke ciki. Kuma ana zargin sunyi ma matan aure da ‘yan mata fyade.
Sun dauki tsawon awanni ukku, tun 12:00am har 3:00am suna ta asa, ba tare da samun wata tangarda ba.
Jama’a na kokawa ganin yadda maharan suka maida yankin na ‘Yandaka tamkar wurin cin kasuwar su, domin ko kwanakin baya ba da dadewa ba sunje kauyen da magariba sun balle shuguna sun sace wayoyin hannu da kayayyakin masaruhi.
Har zuwa rubuta rahoton nan ba wani bayani daga jami an tsaro akan Lamarin.hade da labarin nan akwai hotunan garin da wasu shagunan da aka Balle

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here