HARIN ƳAN BINDIGA A ƳAR GAMJI TA BATSARI, ABUN YA MUNANA.

A ranar asabar 26-03-2022 mutanen garin ƴar gamji ta ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina suka yi gayya tare da rakiyar jami’an tsaro domin aiwatar da wani aikin gyaran hanyar da ta nufi jibiya daga garin su. Wani daga cikin waɗanda suka halarci aikin ya bayyana ma Katsina city News cewa suna cikin sarar ƙaya da sarƙaƙiya a dai dai wani wuri da ake kira sola ta hanyar Jibiya, kawai sai sukaji harbi daga gabas da kuma yammacin su ba ƙaƙƙautawa. A faɗar shi jami’an tsaro basu iya dakatar da su ba saboda yawan su baya misaltuwa, a haka dai masu rabon tsira suka gudu wasu da dama sun samu raunuka.
Da ƙura ta nutsa an samu gawar mutane huɗu wanda akayi masu sutura a ranar, kashe gari kuma an sake komawa tare da jami’an tsaro aka ɗauko ƙarin gawar mutane huɗu, jimla mutane takwas kenan (8) suka kashe.

A wani labarin kuma ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani mutum mai suna Babangida da matarsa dake zaune a ƙauyen ɗan barau cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari, amma bayan sun tafi dashi daga bisani sun sako matar, sannan ya zuwa haɗa rahotan nan sun buƙaci a biya kuɗin fansa naira miliyan ɗayan sannan su sako shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here