Home Sashen Hausa HARE-HAREN ƳAN BINDIGA A YANKIN BATSARI A WANE HALI AKE CIKI YANZU?

HARE-HAREN ƳAN BINDIGA A YANKIN BATSARI A WANE HALI AKE CIKI YANZU?

Hare-haren ƴan bindiga a yankunan batsari wane hali ake ciki yanzu.

BINCIKE ;HARE-HAREN ‘YAN BINDIGA ;
YANKIN BATSARI WANE HALI AKE CIKI YANZU?

daga Aliyu mustafa                                             @ jaridar taskar labarai

Duk wanda ke bibiyar lamarin tsaro a jihar Katsina ya san irin yadda Batsari ta yi qaurin suna wajen matsalar rashin tsaro, domin mutanen Batsari da kewaye ba za su manta da halin da suka tsinci kansu ba na hare-haren ‘yan Bindiga masu satar shanu da garkuwa da mutane domin karɓar kudin fansa.

A kowane lungu mutum yake zauna a yankin Batsari ya xanxani ayyukan ‘yan bindiga, domin sai da ta kai ga ba dare ba rana duk inda aka hadu da su to sai abin da Allah ya yi, ba lalle ba ne a rabu salin-alin.
Har gonaki suke bin mutane suna qwace masu wayoyi, kudi da shanu da sauransu idan ma sun ga dama su yi gaba da mutum; sai an biya kudin fansa. Wannan ina maganar yanayin da aka shiga a yankin duk da sasancin da gwamnatin jihar Katsina ta yi da su a cikin shekarar da ta gabata.


Akwai wureren da koda ana yi wa mutum kidan qoqari to bai isa ya kai kansa ba; madamar yana so ya wanye lafiya ba a yi ciki da shi ba.
Saboda tsanantuwar matsalar ne mutane har sunaye suke yi wa wasu wuraren wanda da ka ji sunan wani wurin to ba sai an gaya maka ba. Misali akwai wani wuri a kan hanyar Batsari zuwa Madogara da ake kira “second sambisa” ma’ana sambisa ta biyu, wurin yayi kaurin suna wajen ayyukan ‘yan bindiga domin sai da ta kai kullum sai sun tarbe mutane sun qwace masu babura, wayoyi da kudi da ma dai duk wani abin amfani da suka samu.


Sai da ta kai manoma ba sa zuwa gonakansu da nufin aikin gona ko gewaya, an qwace shanun noma da yawa a wajen. Duk wannan yana faruwa ne da rana kata ba da dare ba. Dole ya sa masu gona a ire-iren wadannan wuraren suka haqura da cigaba da ayyukan gona. Akwai gonakan da tunda aka yi shuka ba a sake je masu ba.
Bincikenmu ya gano cewa wasu matasan Fulani dake yankin (Safa, Huntaye da Rumawa) ne suka addabi mutane Daga cikinsu akwai; Bishir halba-halba, Lawal Dogon Soja, Dahiru Waya, Dumbaduwa da Kabiru Mai ‘yan tsaki.
Haka lamarin yake a yankin Xangeza; inda suke tsayawa daidai qoramar Kungurum suna karve ma mutane dukiyoyi.
Yankin Shekewa ma duk maganar daya ce. Amma cikin taimakon Allah maji roqon bayinsa, ya karva addu’ar da mutane ke yi da nufin neman sauqin wannan halin da suke ciki. Ya zuwa yanzu duk wuraren da muka lissafa a sama, mutane na zurga- zurga da mu’amulolinsu ba tare da wata matsananciyar fargaba ba. Domin kafin haxa wannan rohoton wakilinmu ya yi tattaki zuwa wasu daga cikin wuraren, har ma ya xauko mana hotunan wurin da ake kira ‘second’ sambisa, inda kuma ya dauko hotunan mutane suna ayyukansu, masu tafiya zuwa qauyukan dake yankin suma suna tafiyarsu a tsanake ciki har da mata da yara qanana. Da muka zanta da mazauna yankunan, sun bayyana mana irin yadda abun yake a da da kuma yanzu , kamar dai yadda muka labarta maku a sama.
Sai dai wasu na kukan cewa lamarin dai sauqi aka samu ba dainawa suka yi ba kwata kwata. Koda yake sun ce mana suna ganin tasirin addu’ar da suke kullum domin ko ‘yan kwanakin nan ba da jimawa ba wasu daga cikin waxanda suka addabe su sun sheqa barzahu sakamakon fadace-fadace da suke yi tsakaninsu. Sannan akwai wani wanda qanensa ya harbe cikin makon jiya. Sun bayyana mana a da ba sa kwana gidajensu sai daji ko wata mafaka kuma kowanne dare sai sun ji amon bindigu na tashi; amma yanzu akan dauki kwanaki ba su ji haka ba, kuma dai duk a gidajensu suke kwana.


Amman yanzu wata sabuwar matsala da ta kunno kai ita ce ta barnar amfanin gona da Fulani ke yi masu. Yankunan Garin Labo, Shingi Tsohuwa da Shingi Sabuwa, Shekewa da sauransu sun bayyana mana irin yadda Fulani makiyaya ke tura masu shanu cikin gonakansu.
Sun ce Fulani suna zuwa su zagaya gonakansu, su zavi wacce ke dauke da wake ko dawa mai nagarta sannan su kora shanu su kiyaye amfanin sarai, daga nan kuma sai su nufi ta gaba. Da muka tambaye su wane mataki kuka dauka kansu? Sai suka ce babu abin da za su iya yi domin duk masu wannan barnar sukan zo da bindigogin Bature sababbi fil cikin izza suna jira ka ce qyas su hau kanka.
Da haka ne suke kira ga gwamnati da ta duba wannan lamari ta yi abin da ya dace.
Satin da ya gabata an samu wani Hari a garin shirgi inda wasu sukace su shidda. Mun kawo cikakken labarin a shafukan mu na jaridar taskar da katsina city news.
Wannan bincike ne na Musamman da jaridun suka gudanar akan halin da tsaro ke ciki a yankin Batsari ta jahar katsina a yanzu.
________________________________________________
Taskar labarai da katsina city news da the links news suna a bisa shafukan. Www.taskarlabarai.com. da www.thelinksnews.com da kuma www.katsinacitynews.com. duk sako ta Kira waya ko whazzap a aiko ga 07047777779

Advertisement:GREENTIDE AGRO
Advertisement:GREENTIDE AGRO

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here