Har yanzu shafin intanet na ‘yan sandan Najeriya ba ya aiki

Kusan kwana biyu bayan masu kutse sun kai wa shafin intanet na ‘yan sandan Najeriya hari, har yanzu shafin ba ya aiki, yayin da ake ci gaba da zanga-zangar neman kawo ƙarshen rundunar SARS.
Shafin mai adireshi www.npf.gov.ng, har yanzu na garƙame kuma da zarar mutum ya buɗe shi zai ce masa “This Account has been suspended” wato “An dakatar da wannan shafin”.
Wannan hari ɗaya ne daga cikin waɗanda aka kai wa sauran shafukan intanet da kuma na sada zumuntar wasu daga cikin hukumomin Najeriya.
Tun a ranar Alhamis masu kutsen suka ƙwace shafin Twitter na Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta NBC.
Wani gungun masu kutse mai suna Anonymous ya yi ikirarin karɓe iko da shafukan domin taya ‘yan Najeriya zanga-zangar neman yin gyara kan ayyukan rundunar ‘yan sandan ƙasar.
Gungun Anonymous ya rubuta a shafin Twitter na NBC ranar Alhamis cewa: “Mu Anonymous mun ƙwace iko da dukkanin shafukan gwamnatin Najeriya domin taya ‘yan Najeriya zanga-zangar #ENDPOLICEBRUTALITY. Muna tare da ‘yan Najeriya.”