Ziyarar Bola Tunubu a Katsina

Gwamna Aminu Bello Masari ya kara bayyana rasuwar Dokta Rabe Nasir a matsayin babban rashi duba da yadda yake da jajircewa tare da sadaukarwa a kan hidima da al’amurran da suka shafi al’umma.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yau a babban dakin taro na Gidan Janar Muhammadu Buhari fadar Gwamnatin Jihar Katsina, a yayin da yake jawabi bayan karbar bakuncin Sanata Bola Ahmed Tinubu da tawagar shi, da suka zo domin yi wa al’umma da Gwamnatin Jiha ta’aziyyar rasuwar marigayin da kuma sauran al’umma da aka rasa sanadiyyar hareharen ta’addanci a wurare daban daban a fadin jihar nan.

Gwamnan ya kara da cewa marigayin yayi duk abinda ya kamata yayi domin ganin nasarar Gwamnati da jam’iyyar APC a wannan jiha, tare da kara yin addu’ar Allah Ya gafarta mashi kurakuran shi.

Alhaji Aminu Bello Masari wanda ya dauki lokaci yana bayanin halin da Jihar take ciki ta bangaren tsaro tare da irin matakan da gwamnatin take dauka, wanda suka hada da gyaran dokar kananan hukumomi domin shigar da Masarautun mu tare da basu rawar takawa cikin samar da tsaron da kuma sauran lamurran da suka shafi al’umma.

Tun farko a nashi jawabin, tsohon Gwamnan Jihar Ikko, jagoran jam’iyyar APC na kasa wanda kuma ke rike da sarautar Jagaban Borgu, Sanata Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa Gwamna Masari cewa yazo Katsina ne domin jajantawa tare da ta’aziyya bisa rasuwar Dokta Rabe Nasir wanda akayi wa kisan gilla da kuma sauran al’ummar da aka rasa sanadiyyar hareharen ta’addanci.

Asiwaju ya kara da cewa Gwamna Masari ya taba gabatar mashi da Marigayi Dokta Rabe a matsayin daya daga cikin kashin gwamnatin APC a jihar Katsina. Sai ga shi cikin kaddarawar Allah, bai rayu har zuwa karshen wa’adin gwamnatin ba na wannan karon.

Yayi addu’ar Allah Ya jikan shi kuma Yaba iyalai da sauran dangi hakurin jure wannan rashi.

Ya bayyana cewa hakika kasar nan tana cikin halin jarabawa kuma in Allah Yaso za muci wannan jarabawa. Ya yaba ma Shugaba Muhammadu Buhari bisa hobbasan da yake tayi wajen tabbatar da an samar tare da biyan duk bukatun jami’an tsaron kasar nan domin kare lafiya da dukiyoyin al’umma. Haka kuma ya jinjina ma Gwamnatin Jiha karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari da kuma al’ummar jihar bisa dagewa wajen yakar ta’addanci.

A cikin wannan tawaga akwai tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Kashim Shattima sai Sanata Abu Ibrahim da kuma Alhaji Nuhu Rubadu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here