…Za’a iya shigowa da Taliya, Makaroni, Wake, Aya, Dabino da Atamfa Motoci da sauran su

Daga Comr Abba Sani Pantami

Idan baku manta ba, a ranar 22 ga wannan watan gwamnatin Najeriya ta bude iyakokin kasar guda hudu a kowacce shiyya ta kasar na jihohin Katsina, Kebbi, Rivers Da Ogun.

A jiya Litinin aka gudanar da bukukuwan bude iyakokin, inda manyan jami’ai, sarakuna Dattawan garuruwan da sauran al-umma suka cika a wurin bikin.

A yayin gudanar da bikin manyan jami’an hukumar kwastam sun yiwa Al-ummar yankunan bayani dallah-dallah kan irin kayayyakin da aka bawa al-umma umurnin shigowa da su Najeriya.

Wasu daga cikin abubuwan da gwamnatin kasar ta yadda a shigo dasu gasu kamar haka;

Taliya
Makaroni
Wake
Aya
Dabino
Atamfa
Motoci da sauran su.

Dukkannin wa ‘yan nan abubuwan an yadda a shigo dasu, amma da sharadin dole sai ka biyawa kowane daga ciki haraji.

Abubuwan da gwamnatin kasar har yanzu ta haramta shigowa da su gasu kamar haka;

Shinkafa
Gwanjo
Mai Na Abinci

Al-ummar yankunan sun nuna matukar farin cikin su kan bude iyakokin kasar da aka yi, wanda hakan zai basu dama su cigaba da gudanar da kasuwancin su duk da suna cikin matsalolin rashin kudi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here