Jam’iyyar APC ta gamu da cikas kan shirinta na fara sayar da fom din takara domin darewa kujerun siyasa a zaben 2023 a ranar Asabar.

Masu neman darewa kan madafun iko a karkashin inuwar jam’iyyar a zaben 2023 dai sun yi cirko-cirko a hedikwtar jam’iyyar ta kasa, ganin cewa ba a fara sayar da takardun ba kamar yadda aka tsara.

Wata majiya mai tushe a jam’iyyar da ta nemi a boye sunanta ta ce, “Hakan ya faru ne saboda dan kwangilar da aka bai wa aikin buga takardun bai kawo su ba, watakila ya kawo kafin a gama hutun karshen mako.

“Idan har hakan ta faru, za a iya fara sayar da fom daga ranar Litinin ko Talata.

“Kwamitin Gudanarwar Jam’iyya na Kasa ne zai yanke shawara kan sabon lokacin.”

To sai dai duk yunkurin ji ta bakin Sakataren Yada Labaran Jam’iyar APC na Kasa, Felix Morka, bai amsa sakonnin da aka tura mishi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here