Ana dakon yanke wa El-Zakzaky hukunci

Jami'an tsaro a bakin aiki

An jibge jami’an tsaro a wajen kotun da ke sauraron karar da ake yi wa shugaban kungiyar Harka Islamiyya ta mabiya mazahabar Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, a jihar Kaduna.

'Yan jarida a wajen kotu

An hana ‘yan jarida shiga harabar kotun, bare kuma zauren da ake shari’ar, inda suka yi rukuni-rukini domin jiran tsammani.

Kotu ta dawo daga hutun rabin lokaci, inda za a ci gaba da sauraren zaman. Ana kuma sa ran nan ba da jimawa ba, Malamin da maidakinsa za su san makomarsu.

El-Zakzaky da maidakinsa Zinatu a cikin motar jami'an tsaro

Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tare da maidakinsa Zinatu sun iso kotu a cikin motar shiga-ba-biya ta jami’an tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here