Daga bishir suliman  @katsina city news

Hangen Dala Ba Shiga Birni Ba: Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kafa Kutunan Sauraren Karar Zabe.

Biyo bayan korafe – korafe da babbar jam’iyyar Adawa PDP ta yi a kan zaben ƙananan Hukumomi a jihar Katsina, wanda ya gudana a ranar 11 ga watan da muke ciki.

Jam’iyyar PDP ta kalubalenci sakamakon zaben da kuma korafe-korafe na rashin kafa kutunan jin koke zabe, wanda hakan ta sha alwashin garzaya wa kuto don neman hakkin ta.

Inda a yau babban jojin jihar Katsina, Maishara’a Musa Dalladi Abubakar, ya kaddamar da kotunan sauraran kararrakin zaben, a daukacin shiyyoyi uku na jihar nan, amma yankin Funtua za su gudanar da zamansu a cikin ƙwaryar Katsina sakamakon wasu dalilai.

An rantsar da Alkalai da kuma mataimakan da za su jagoranci gudanar da shara’ar a yankin Katsina da Daura da kuma Funtua.

Daga Bishir Suleiman Katsina City News

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here