Home Sashen Hausa Halin Da Na Bar Rundunar Soja Yanzu, Yafi Yanda Na Sameta Inganci...

Halin Da Na Bar Rundunar Soja Yanzu, Yafi Yanda Na Sameta Inganci – Buratai

Halin Da Na Bar Rundunar Soja Yanzu, Yafi Yanda Na Sameta Inganci – Buratai

Tsohon Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya Laftanar-Janar Tukur Buratai mai ritaya ya ce halin da ya bar Rundunar ya fi yadda ya same ta inganci nesa ba kusa ba.

A jawabinsa yayin bikin faretin yi masa bankwana bayan ya mika ragamar Rundunar ga sabon Shugabanta, Manjo-Janar Ibrahim Attahiru, Buratai ya ce Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta samu dimbin nasarori a yaki da ta’addanci da sauran kalubalen tsaro a karkashin jagorancinsa.

Ya ce shugabancinsa ya tabbatar da ganin cewa ta inganta jin dadin sojoji ta kuma ba su isasshen horo da kwasa-kwasai domin kara musu kwarewa a aikinsu na bakin daga.

Ya ce duk da cewa babu makawa wata rana sai an rabu da juna, ya rasa irin kalmomin da suka fi dacewa da zai yi amfani da su ya yi wa hazikan sojojin da jami’an Rundunar da suka yi aiki da shi bankwasa.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here