Advert
Home Sashen Hausa Halin Da Ake Ciki A Nijeriya: "Dole Ne Mu Zauna Mu Ga...

Halin Da Ake Ciki A Nijeriya: “Dole Ne Mu Zauna Mu Ga Ya Za Mu Samar Wa Kanmu Mafita.” -Shehu Dahiru Usman.

Halin Da Ake Ciki A Nijeriya: “Dole Ne Mu Zauna Mu Ga Ya Za Mu Samar Wa Kanmu Mafita.” -Shehu Dahiru Usman.

Daga A.I Musa. @Katsina City News

An bayyana hadin kai da tashi tsaye a matsayin hanya daya tilo da za ta samar da mafita daga halin da ake ciki na tsanani da wahalar rayuwa a Najeriya.

Shahararren Malamin addinin Islama na darikar Tijjaniyya a Nijeriya, Shehu Dahiru Usman Bauchi wanda ya samu wakilcin dansa Sayyadi Naziru Dahiru Usman Bauchi ne ya bayana haka a lokacin da yake gabatar da wani jawabin dare na ‘Makon Hadin Kan Musulmi’ wanda ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka shirya a ranar Asabar din nan a Katsina.

“Yanzu kasar nan ana cikin yunwa, ana cikin talauci, ana cikin ‘insecurity’. ‘Kidnapping’ ya yi yawa, fashi da makami ya yi yawa, kashe-kashe ya yi yawa, zalunci ya yi yawa. Ana danne mutane, ana wahalar da su, abinci ya yi tsada…shikenan kawai sai mu tsaya mu yi ta cewa Allah ya kawo sauki?” Ya yi tambaya.

Ya ci gaba da cewa; “Dole mu zauna mu yi tsari mu ga yadda za a yi, wace hanya za mu bi mu kawo waraka na wannan matsaloli.”

Ya kara da cewa; “Babu wanda zai zo daga wata duniya ya gyara mana Nijeriya sai mu ‘yan Nijeriyar da kanmu.” Ya ankarar.

“Kasashen da suka gyaru din ma, ba wai wasu ne suka sauko daga sama kamar ruwa suka zo suka gyara masu ba; sai da aka samu wasu jajayen wuya, jajirtattu, masu tunani da hikima da basira suka zo suka kawo gyara.”

Ya ce, zuwan tura ne farkon abin da ya kirkiro akidodin kafurta musulmi a wannan kasa da wannan nahiya tamu, “don haka lokaci ya yi da za mu aje sa6ani a tsakaninmu da bambance-bambancenmu mu yi wa juna uzuri mu hada kai a karkashin kalmar Allah mu yi karfi mu dage mu ga cewa mun kauda duk abin da ba mu son shi wanda yake cutar da al’ummarmu.”

Sayyadi Naziru ya kuma kara nunasshe da musulmin wannan kasa cewa; ba fa ranar da za su samu ‘yancin kansu da mutuncinsu sai sun dawo wa karantarwar addininsu na musulunci da neman ilimi a kowane fanni, inda ya ce wannan ne babban abin da zai dawo da darajar al’ummar musulmi ba na wannan kasa kadai ba, har ma da duniya baki daya.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...