Saboda warware rudu da hayaniya da wata magana ta haifar kwanakin nan kan Halifancin Tijjaniyya a Najeriya, Babban Halifan Tijjaniyya Na Duniya kuma Halifan Sheikh Ibrahim Nyass, wato Khalifa Sheikh Mahy Sheikh Nyass, ya tabbatar da cewa su daga can Kaulaha ba su turo kowa wajen kowa ba kan maganar Halifancin Tijjaniyya a Najeriya.
Ya yi wannan jawabin ne yayin Liyafar cin abincin dare da Gwamnan ya gayyace shi da a ka yi yau Alhamis, a dakin taro na Africa House, a fadar gwamnatin Jihar, a Kano.
Ya ce wancan abinda a ka yi ba haka ya kamata ya zama ba, “A wannan kasa ta Najeriya da wannan Jiha ta Kano mai albarka akwai manya kuma bijiman Shehunai. Akwai manyan shugabannin Zawiyyoyi. Sannan akwai Manyan Limamai da ya kamata a tuntuba. Amma ba ai haka ba.”
“Mu dai ba mu ce kaza ba. Kuma ba mu ce kowa ya zo ya ce kaza ba,” in ji shi.
Sannan saboda irin tarbiyya da Shehun ya samu daga gida, duk da cewar ya ce su ba su turo kowa daga Kaulaha ba domin ya fadi wani abu da ya shafi waccan magana, sai ya ce “Abinda zan ce shine waccan magana ba a fade ta yadda ya kamata ba. Ba a fade ta Bisa hanya mikakkiya ba.”
Ya yi wa Gwamna addu’ar samun kariya daga magabta da kuma samu karin lafiya. Ya ce “Allah Ya kare ka daga dukkan abin ki. Mun ga yadda kake taimakon Addinin Musulunci da kuma Dariqar Tijjaniyya. Allah Ya saka maka da mafificin alheri.”
A na sa jawabin Gwamna Ganduje ya yabawa da Shehun kan ziyarar da ya kawo jihar Kano da gidan gwamnatin Jihar Kano. Ya kara da cewa “Irin wannan ziyara ta na kara karfafa zumuncin da ke tsakaninmu da ku, wadannan manyan bayin Allah.”
“Ina mai farin cikin sanar da Halifa cewar, ‘yan Dariqar Tijjaniyya su na da muhimmancin gaske a wajenmu. Mu na da su da yawa a cikin wannan gwamnatin ta mu. Kuma Alhamdulillah sun rike mana amana yadda ya kamata,” in ji Gwamnan.
Gwamna Ganduje ya kuma tunatar da yadda danganta take mai karfi da girmama juna tsakanin gwamnatin Kano da Marigayi Sheikh Ishaqa Rabi’u Khalifa. Ya ce “Lokacin ya na raye haka muke zuwa a kai a kai domin domin neman madadi da albarka. Allah Ya jikansa da Rahama.”
A wajen taron akwai kwamishinoni da manyan masu ba Gwamna shawara da dattawan jam’iyyar APC da ya’yan Sheikh Ibrahim Nyass da jikokinsa kimanin su Talatin da manyan jagororin Dariqar Tijjaniyya a Najeriya da kuma manyan Limamai da manyan Muqaddamai da
Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here