Hadimin Ganduje Ya Gwangwaje Matasa Da Tallafin Jakuna
Mai bai wa gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin matasa, Murtala Gwarmai, ya gwangwaje wani matashi a jihar da tallafin jaki a ranar Alhamis.

Gwarmai, ya rabawa matasan kayan tallafin da suka hada da jaki da babura da kekunan hawa ga wasu marayu da dai sauran su
Gwarmai, ya rabawa matasan Babura masu kafa biyu da kekunan hawa da kudin naira dubu 100 wasu kuma sun rabauta da bulo 500 da bandiran Kwanan rufi 5 da wani matashi da ya amfana da jaki da dai sauran su.



Rahotanni sun nuna cewa yayin raba tallafin wanda ya gudana a ma’aikatar matasa da wasanni ta jihar Kano, akalla matasa 40 ne suka amfana da rabon kayan tallafin.
Hadimin ya ce matashin da ya amfana da tallafin jakin, shi ya bukaci a bashi tallafin jakin don ya inganta sana’arsa ta safarar kayan gini da suka hada da Kasa da Yashi da Dutse da Bulo da dai sauransu.
Matasan da suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikinsu a fili tare da godewa mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin na matasa.