Advert
Home Sashen Hausa Haɗa Hoton El'zakzaky da Yari: Marafa yayi Allah wadai da amfani da...

Haɗa Hoton El’zakzaky da Yari: Marafa yayi Allah wadai da amfani da addini wajan yarfen siyasa a Zamfara

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Ganin yadda wasu suka fito da sabon salu na yarfen siyasa bayan kage da kazafi da bata suna,yau Kuma an fito da salun amfani da addini a matsayin kayan siyasa, abubuwan da ke faruwa a jihar Zamfara a baya-bayan nan sun wajabta kiran a daina alakanta siyasa da rashin tsaro da addini.

Wannan Kiran Yana Yana dauke ne cikin wata takarda Mai dauke da sa hannun kakakin Jam’iyar APC bangaren Sanata kabiru Marafa a jihar Zamfara,
Hon. Bello Bakyasuwa Maradun.

Ya kara da cewa yarfen siyasa ta amfani da Bangaren addini,na baya-bayan nan shi ne hada hotunan tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari Abubakar da wasu masu yi masa biyayya tare da Mal. Ibrahim Zak-Zaky wanda aka baje kolinsu a wurare masu mahimmanci a cikin jihar.

Ya ce abin da muka fahimta shi ne, “wannan wani aiki na matsorata na kulla alaka ta karya tsakanin tsohon Gwamna da jagoran Shi’a domin a samu sauki a siyasance don haifarda gaba daga jama’a da kungiyoyi.

Marafa yace idan ba’a manta ba a farkon makon da ya gabata ne wata sanarwa daga wani da ya bayyana kansa a matsayin magatakardan jam’iyyar APC na bangaren gwamnati ya zargi Janar Aliyu Gusau da taimakawa ‘yan fashi da makami, munyi Allah wadai da matakin tare da nesanta kanmu da wannan magana saboda yunkurin alakanta ta da Jam’iyyar da mu masu ruwa da tsaki ne a kanta da kuma girmama dattijon da ya dace duk da cewa mun fito daga jam’iyyu mabanbanta.

Ya ce a baya wasu zarge-zargen da aka yi da kuma bayyana su a kan marigayi Hon. Muttaka Rini da Dauda Lawal Dare dukkansu sun fito ne daga sansanonin ‘yan adawa na jam’iyyar APC wanda duk muna ganin abin Allah wadai ne.

An Kuma sake fito da wannan zargi da yarfen daga Majalisar Dokokin Jihar, an tuhumi wasu ‘yan majalisa biyu na Bakura da Anka da laifin taimakawa ‘yan fashi da makami tare da dakatar da su daga majalisar ba tare da sauraren shari’a ba.

Muna kira na musamman ga Malaman Addinin Musulunci da su tashi tsaye wajen yin wa’azi kan zarge-zarge da ake yi wa mutane domin Musulunci da Shari’ar da aka san Jihar da su sun tsaya kyam a kansu.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

10 ROAD REHABILITATION PROJECTS COMPLETED IN KEBBI STATE!

#PositiveFactsNG Do you know that the Buhari administration has just concluded the rehabilitation of 10 roads in Kebbi State under the Special Maintenance, Repairs and...

Ba abinda zai dawo da ni harkar siyasa — Obasanjo

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo a ranar Asabar ya sake jaddada ƙudurinsa na ficewa daga harkokin siyasa, inda ya ce babu abin da zai...

CONSTRUCTION OF THE BARO – MINNA RAIL LINE IS SET TO COMMENCE!

#PositiveFactsNG To maximise the business opportunities that the Baro Seaport will unleash when completed, do you know that the Buhari administration has recently awarded the...

Al’uma ciki da wajen Najeriya suna tururuwa zuwa ta’aziyyar rasuwar Mahaifiyar Alhaji Ɗahiru Mangal: Tsohon Shugaban ƙasar Nijar, da Gwamnan Kano sun sun isa...

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya jagoranci tawagar Gwamnati zuwa ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar hamshakin dan kasuwa, Alhaji Dahiru mangal...

ZUWAN DALLAZAWA SAFANA, DA ASALIN GIDAN YARIMA DAKE CIKIN BIRNI KATSINA.

Dallazawa sune zuri'ar Malam Ummarun Dallaje. Ummarun Dallaje kamar yadda Tarihi ya nuna shine Sarkin Katsina na farko daga tsatson FULANI, Kuma daga cikin...