Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sake dakatar da jirage daga Najeriya

Hadaddiyar Daular Larabawa

Hadaddiyar Daular Larabawa ta sake dakatar da zirga-zirgar jirage zuwa da dawowa daga Najeriya, sa’o’i 48 bayan dage haramcin farko.

Kwamitin Koli na kare aukuwar bala’o’i na kasar ne ya sanar da bada damar ci gaba da jigilar fasinja tsakanin kasashen biyu a shekaran jiya Asabar, bayan watanni da dama na haramcin.

A cikin sanarwar da aka fitar ta shafin yanar gizona gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa, an sanar da tsare tsaren tafiye-tafiye ga fasinjojin da ke shigowa daga Afirka ta Kudu, da Najeriya da Indiya.

A cikin sanarwar, an bukaci fasinjoji da su “gabatar da sakamakon gwajin korona da ke nuna cewa ba sa dauke da cutar awanni 48 kafin tashin su.”

Bugu da kari “Dole ne ya kasance an yi gwajin a wuraren da aka amince da su ”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here