Gwamnatina Ta Dauki Ma’aikata Fiye Da Dubu Huɗu Cikin Shekara Shidda, Cewar Gwamna Aminu Masari

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta dauki ma’aikatan sama da dubu hudu a hukumomi da ma’aikatun jihar Katsina cikin shekara shidda da suka wuce.

Gwamna Masari ya bayyana haka, a bikin ranar ma’aikata ta duniya a ranar Asabar data gabata, bakin shugaban Ma’aikatan Jihar Katsina, Alhaji Idris Tune da ya wakilcin gwamnan a dakin taro na hukumar kula da Ma’aikatan kananan hukumomin jihar Katsina.

Ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen inganta rayuwar jin dadin Ma’aikatan Jihar kuma za’a ci gaba da bunkasa rayuwar su da ta aikin su.

Tun farko shugaban Kungiyar Kwadago Ta Jihar Katsina, Alhaji Hussani Hamisu ‘Yanduna ya ce rana ce ta musamman ga shugabanni kwadago da membobinta da sauran Ma’aikatan jihar Katsina. Wadanda suka yi bayani akwai babban jojin jiha, Mai Shari’a, Musa Danladi Abubukar da sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa da Shugaban Kungiyar Yan kasuwa, Muntari Abdu Rumah da kuma Dr. Al’maiki Hassan Rafin Dadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here