Gwamnatin Zamfara ta samar da rumbun ajiyar gwal

Jihar Zamfara dake arewacin Najeriya tana da zarzikin zinare karkashin kasa da yafi sauran jihohi.

Gwamnatin Zamfara ta samar da rumbun ajiyar gwal

Zinari
Zinari yana daya daga cikin ma’adanin kasa mafiya daraja.

Gwamnatin jihar Zamfara ta gina Rumbun adana zinari

Gwamnatin Jihar Zamfara a arewacin Najeriya ta ce ta ƙaddamar da rumbun ajiyar gwal nata na kanta domin rage dogaro kan Gwamnatin Tarayya.

Kwamishinan Kudi na Jihar, Alhaji Rabiu Garba ya faɗa wa manema labarai a Gusau ranar Talata cewa “duk da cewa gwamnati ta hana haƙar ma’adanai a jihar, mun samu damar sayen gwal ɗin daga hannun ‘yan kasuwar da ke da lasisi”.

Zinari shine mafi girman darajar ma'adinan ƙasa.
Gwamnatin Zamfara zata samar da Rumbun adana zinari.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito shi yana cewa: “Ya zuwa yanzu, muna da gwal mai nauyin kilo 30 kuma za mu ci gaba da gina shi kamar kowacce ƙasa, mu ma za mu samar da rumbun ajiyar ma’adanai kuma namu zai kasance na gwal ne.

“Idan aka ɗage haramcin haƙar ma’adanai kuma harkoki suka ci gaba, muna sa ran samun kyautar gwal ɗin daga ‘yan kasuwa sannan kuma Gwamnatin Tarayya ma ta ba mu wani abin.”

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ce za ta ci gaba da kula da shi sannan kuma za a yi amfani da shi ne kawai a lokacin da ya dace.

Gwamnatin Anjeriya ta haramta haƙar ma’adanai a Zamfara tun a watan Agustan 2019 sakamakon abin da ta kira alaƙar da ke tsakanin haƙar ma’adanai da kuma matsalar tsaro a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here