Gwamnatin Zamfara na zargin wasu ma’aikatanta da fashin daji

Gwamna Matawalle

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta bankado wasu ma’aikatan gwamnati da ta yi zargin cewa yan fashin daji ne.

A cewar wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Ibrahim Magaji Dosara ya sanyawa hannu, ma’aikatan na cikin mutum 35 da aka kama a Gusau, babban birnin jihar.

Gwamnatin ta bayyana mamaki kan yadda wasu daga cikin mutanen da aka kama suka kasance ma’aikatan gwamnati.

A cewar sanarwar, tuni aka yi bincike a kan mutanen inda kuma suka tabbatar da yadda suke ba da gudummawa wajen aikata miyagun laifuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here