#GaskiyarLamarinNijeriya

Ko kun san cewa, a ranar 1 ga Disamba, 2015, Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ƙaddamar da masana’antar sarrafa rake ta zamani a harabar Cibiyar Binciken Noma (IAR) da ke Jami’ar Ahmadu Bello a Zariya, wacce ita ce cibiya irinta ta farko a Nijeriya?

An kafa cibiyar masana’antar ne da nufin duƙufa wajen samar da nau’in rake, domin yawaitar ingantacce, tsarkakakke kuma tsaftataccen irin shuka na rake, don bunƙasa fannin sukari a ƙasar.

Ita dai wannan muhimmiyar masana’anta ta haɗin gwiwa ce tsakanin Majalisar Bunƙasa Harkokin Sukari ta Ƙasa da Cibiyar IAR, don magance matsalolin samar da ingantaccen sukari, maras cutarwa, a Nijeriya ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Wannan na daga cikin irin namijin ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaba Buhari ta riƙa yi a ƙoƙarinta na mayar da Nijeriya kan tafarkin dogaro da noma da kuma tsamo ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga cikin ƙangin talauci nan da lokaci kaɗan!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here