Gwamnatin Ogun ta dakatar da kwamishina kan zargin lalata da yarinya

Gwamnatin Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, ta dakatar da Kwamishinan Muhalli na jihar, Abiodun Abudu-Balogun, daga bakin aikinsa, kan zargin cin zarafin wata yarinya ‘yar shekarar 16.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta ce dakatarwar za ta ci gaba da aiki har sai an kammala wani bincike mai zaman kansa da ake yi game da zargin.
Tun da farko labarin ya fito ne bayan yarinyar da ke makarantar sakandare ta saki wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, tana iƙirarin cewa kwamishinan ya nemi cin zarafinta ne a cikin gidansa.
Sanarwar ta ce dakatarwar da aka yi wa kwamishinan ba ta nufin an kama shi da laifi ne, inda ta ce ta yi hakan ne domin samun damar zurfafa bincike kan wannan lamari.
Sai dai cikin wata sanarwa da kwamishinan ya fitar, ya musanta zargin inda ya bayyana cewa ba shi da hannu a cikin wannan batu.
Duk da cewa bai musanta haduwa da yarinyar ba a gidansa, amma ya ce ba shi da wata mummunar niyya a game da ita. Yana mai cewa kawai ɓata suna ne da ake so a yi masa a siyasance.
Cin razafin mata ba ƙaramin laifi bane a Najeriya, ‘yan kwanakin nan ma sai da mutane suka nuna goyon bayansu kan a riƙa yi wa waɗanda aka ci zarafinsu adalci.
A shekarar da ta gabata ne mutane a ƙasar suka yi wata zanga-zangar nuna ƙin jinin masu fyaɗe ko kuma cin zarafin mutane.