Gwamnatin Nijeriya Za Ta Fara Aiki Da Fasahar 5G, Cewar Ministan Sadarwa Sheikh Pantami

Daga Comr Abba Sani Pantami

Ministan Sadarwa da raya tattalin Arziki na Digital Sheikh Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sanar da kudirin gwamnatin Nijeriya na fara amfani da fasahar 5G a bangaren sadarwa nan ba da jimawa ba.

Ministan ya sanar da hakan ne ta bakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Nijeriya, NCC, Farfesa Umar Garba Dambatta, a lokacin sa hannu kan wata yarjejejniya tsakanin hukumar tasa da Hukumar Tauraron Dan Adam ta kasar a Abuja ranar Laraba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnati ta ce mutane su kwantar da hankalinsu kan duk wata jita-jita da suke ji dangane da fasahar 5G inda ta ce alfanun fasahar ba zai misaltu ba.

Yarjejeniyar dai sharar fage ce kan samar da kayan aikin kaddamar da fasahar a kasar.

Shugaban Hukumar NigComSat Dokta Abimbola Alale ya ce yarjejeniyar da hukumomin biyu suka sa wa hannu za ta sauya fagen sadarwa da harkokin intanet a Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here