Gwamnatin Najeriya ta kara kudin man Fetur zuwa Naira N212.61 duk lita

Bayan sanarwa da karyata cewa da aka rika yi wai gwamnatin Najeriya za ta kara kudin mai, yanzu dai hakan ya tabbata.

Hukumar dake tsarawa da kyayyade farashin man fetur PPPMC ta bayyana cewa za a rika siyar da lita ɗayan man fetur a gidajen mai naira N209.61 da N212.61.

Wannan sanarwa da hukumar ta fitar a yammacin Alhamis ya girgiza ƴan Najeriya ganin da kanta kamfanin mai ta Kasa ta karyata cewa wai gwamnati zata kara kuɗin mai tun a farkon wannan wata na Maris.

Shugaban kamfanin mai na kasa Mele Kyari ta hannun shugaban sashen hulda da jama’a, Kennie Obateru, ya bayyana cewa kamfanin man ba za ta kara kudin mai ba kamar yadda ake ta yadawa a wancan lokacin.

A lokacin har da yin kurin cewa ba za ta yi haka ba saboda kada Talakawa su tagayyara.

Kowa dai ya san abinda zai biyo baya akan kayan masarufi da kudin shiga motocin haya.

Tun a makon jiya gidajen mai a fadin kasar na suka daina sai da mai a dalilin shirin kara farashin litar mai.

Layukan motoci suka fara bayyana a gidajen mai, a hankali cikin kwanaki biyu sai wahalar mai ya yi tsanani musamman a jihar Legas da babban birnin tarayyar, Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here