Gwamnatin Najeriya ta amince ta miƙa DCP Abba Kyari ga Amurka

Ofishin Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan ranar Alhamis bayan ministan ya gabatar wa Babbar Kotun Tarayya a Abuja buƙatar miƙa ɗan sandan wanda tuni aka dakatar da shi don neman amincewarta.
Antoni janar ɗin ya ce ya nemi a kai Abba Kyari Amurka ne bayan buƙatar da ƙasar ta gabatar masa, inda ya yi amfani da dokar miƙa wanda ake zargi da laifi ƙasashen ƙetare ta Extradition Act a gaban kotun.
Sai dai babu ƙarin bayani a yanzu game da abin da zai faru da sauran zarge-zargen da hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi, NDLEA, take yi masa na safarar hodar ibilis idan aka kai shi Amurka.
Tun a 2021 ne Amurka ta zargi DCP Kyari da mu’amala da Ramon Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi wanda kuma tuni yake tsare a ƙasar, da damfarar wasu kamfanoni fiye da dala miliyan ɗaya.