Gwamnatin Masari Ta Tallafawa Yan Kasuwa 385 Da Iftila’in Gobara Ya Shafa a Central Market.

Gwamnatin Jihar Katsina ta samar da tallafin kayan abinci ga yan kasuwarda Iftila’in gobara ya shafa a babbar kasuwar Katsina.

Kwamishinan Wasanni da Walwalar Jama’a na jihar Alh.Sani Aliyu Danlami ne ya kaddamar da rarraba tallafin a farfajiyar kasuwar.

Kamar yadda kwamishinan ya bayyana,tallafin ya biyo bayan umarni daga gwamna Aminu Masari domin rage wasu daga cikin wahalhalunda yan kasuwar ke fuskanta.

Alhaji sani Aliyu Danlami ya bukaci yan kasuwar akan su kara jajircewa wajen addu’oi akan Allah ya kawo karshen matsalar tsaro dake addabar jiharnan.

A jawabinsa,Shugaban Kungiyar yan kasuwa na Jihar Katsina,Alhaji Mujittafa Lamis Gafai,ya yabawa Gwamna Aminu masari akan Samar da tallafin.

A nashi bangaren,Shugaban kungiyar yan kasuwa na Babbar Kasuwar Alh.Abbas Labaran Albaba ya sanar da yan kasuwar cewa nan ba da jimawa ba zasu dara domin kuwa gwamnatin masari daf take da tallafa masu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here