Gwamnatin Jihar Katsina ta raba tallafin kayan abinci ga mabukata dubu goma, a Jihar domin azumin watan Ramadan.

A ranar alhamis 14/04/2022, Kwamishinan ma’aikatar kula da harkokin wasanni walwala da jin dadin jama’a na Jihar Katsina Hon. Sani Aliyu Danlami ya Jagoranci kaddamar da raba kayan tallafin amadadin Gwamnatin Jihar.

Kayan tallafin abincin da aka raba ma mabukatan wanda akasarinsu mata ne, sun hada da buhun nan gero, buhun nan dawa da buhun nan masara.

Da yake gabatar da jawabinsa yayin da yake kaddamar da raba kayan tallafin, Hon. Sani Aliyu Danlami ya bayyana cewa” Mai girma Gwamna Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya bada umurnin raba tallafin ga mabukata.

Domin rage radadi musamman wannan wata da muke ciki na azumin watan Ramadan. Daga karshe ya gargadi wadanda su ka amfana da tallafin da suyi amfani da shi, domin bana saidawa bane.

Kwamishinan ya cigaba da cewa” za a raba tallafin ga mabukata mata dubu biyu, a cikin garin Katsina, yayin za a raba ma mabukata dubu takwas a kananan hukumomin dake fama da matsalar tsaro a Jihar Katsina.

Wadanda su ka amfana da tallafin sun nuna farin cikinsu tare da godiya akan wannan tallafi da aka basu, inda su ka bayyana cewa” wannan tallafi zai taimaka masu kwarai da gaske wajen rage masu radadi musamman wannan lokaci na azumin watan Ramadan.

Taron kaddamar da raba tallafin da aka gudanar a tsohon gidan Gwamnatin Jihar Katsina ya samu halartar Shugaban hukumar bada agajin gaugawa ta Jihar Katsina Hon. Babangida Nasamu, da wasu daga cikin Daraktocin hukumar.

14 April, 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here