Advert
Home Sashen Hausa Gwamnatin Katsina ta bada tallafin kudi ga wadanda harin 'yanbindiga ya shafa...

Gwamnatin Katsina ta bada tallafin kudi ga wadanda harin ‘yanbindiga ya shafa a Batsari da Matazu…

Gwamnatin jihar Katsina ta bada tallafin N50,000 ga dukkan wadanda harin yan bindiga ya rutsa da su a kananan humumomin Batsari da Matazu.

Da yammacin yau lahadi 14/11/2021,

Shugaban kwamitin kula da yan gudun hijra da wadanda wani ibtila’i ya shafa kuma Kwamishinan ma’aikatar kula da harkokin wasanni walwala da jin dadin jama’a na jihar Katsina Hon. Sani Aliyu Danlami ne gabatar da taimakon ga mutanen da ibtila’in ya shafe lokacin da ya ziyarce su a asibitin kwararri ta Gwamnatin tarayya dake a jihar Katsina domin duba su.

Kamar yadda muka samu, akalla mutum goma sha tara ne (19) suke kwance a asibitin suke amsar magani inda mutum (12) daga cikinsu, sun fito ne daga garin Batsari dake cikin karamar hukumar Batsari, yayin da sauran mutum (7) su ka fito daga garin Gwarjo dake cikin karamar hukumar Matazu.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanakin baya ne ‘yan ta’adda dauke da makamai suka kai hari garin Batsari da kuma garin Gwarjo na karamar hukumar Matazu wanda yayi sanadiyya mutuwar mutane da dama tare da man raunata wasu.

Da yake jawabi jim kadan bayan bayar da tallafin, Hon Danlami Ya bayyana cewa “Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari zata cigaba da kula da lafiyarsu har a sallame.”

Ya kuma kara da cewa “Gwamnatin zata kai tallafin abinci ga iyalan da wannan ibtila’i ya shafa a garuruwansu.”

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...