A zamanta na yau Laraba 20 ga watan Oktoba 2021, Majalisar zartaswa ta jiha karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta amince da gina gadojin kasa (underpass) a mahadun dake Kofar Kaura da kuma Kofar Kwaya dake nan babban birnin jihar.

Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri Alhaji Tasi’u Dahiru Dandagoro ya bayyana haka bayan kammala taron Majalisar a Gidan Janar Muhammadu Buhari fadar Gwamnatin Jihar Katsina.

Alhaji Tasi’u ya bayyana cewa wadannan ayyuka da aka kiyasta za suci kudi sama da Naira Miliyan Dubu biyar, kamfanin gina hanyoyi na Triacta Nigeria Limited zai gina su cikin watanni goma sha biyu idan Allah Ya yarda.

A daya bangaren, Kwamishinan Albarkatun Ruwa Alhaji Musa Adamu Funtua ya bayyana cewa Majalisar zartaswas ta kuma amince da a bada kwangilar fadada Madatsar ruwa ta Ajiwa domin kara yawan ruwan da take ajiyewa domin tacewa da halbawa zuwa cikin garin Katsina da kewaye.

Kwamishinan ya kara da cewa wannan aiki na cikin jerin ayyukan da Gwamnatin ta tsara take kuma aiwatarwa daya bayan daya domin samar da isashshen ruwa ga birnin Katsina da kewaye.

Kwamishinan Kasafin kudi da Tattalin arziki Alhaji Faruk Jobe ya bayyana cewa wadannan ayyuka suna kunshe cikin kasafin kudi na shekarar 2022 mai kamawa.

Bayan kammala wannan taro, Gwamna Aminu Bello Masari ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Marigayi Dr Ishaq Kurfi wanda ya rasu ranar Litinin da ta gabata.

Gwamnan wanda Sanata Umar Kurfi ya tarba, ya roki Allah Ya jikan shi da gafara kuma Yaba iyalai da sauran dangi hakurin jure wannan babban rashi.

Daga nan sai Gwamna Aminu Masari ya wuce tashar bunkasa karfin yadda ruwa ke shigowa gari (booster station) da take a gidan ruwa na Kofar Kaura domin yadda aikin canza manyan famfunan dake halba ruwan zuwa babban tankin dake kan shataletalen gidan rodi da wanda yake a Rafindadi da kuma sauran hanyoyin ruwa daban daban na cikin gari da kewaye.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa Alhaji Musa Adamu Funtua da Shugaban kamfanin Continental dake aikin kwangilar Alhaji Salisu Mamman suka zagaya da Gwamnan wajen duba wannan aiki.

Mataimakin Gwamna Alhaji Mannir Yakubu da wasu manyan jami’an Gwamnatin Jiha suka rufa wa Gwamnan baya a wannan ziyara.

Muna rokon Allah Ya yaye mana masifun da suka addabe mu, musamman ta’addanci.

Ya Allah Ka jikan duk wadanda suka rasa rayukan su ta hanyoyi mabanbanta Ka yafe masu kurakuran su, mu kuma Allah Ka bamu ikon cikawa da Imani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here