YANZU-YANZU: Gwamnatin Kano ta rufe makarantar da a ka binne Hanifah

Gwamnatin Nijar Kano ta bada umarnin rufe Noble Kids Academy, makarantar kuɗi da ke Kwanar Dakata, inda a nan ne Abdulmalik Tanko, wanda ya yi garkuwa da Hanifah Abubakar, ƴar shekara 5, ya kashe ya kuma binne ta.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a jiya da daddare ne dai dubun Tanko ta cika, wanda shine malamin Hanifah a makarantar, amma ya sace ta ya kuma hallaka ta bayan ya karɓi wani kaso na naira miliyan 6 da ya nema a matsayin kuɗin fansa.

Da ya ke sanar da rufe makarantar na gaggawa a yau Alhamis, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Muhammad Sa’idu Ƙiru, ya ce za a rufe makarantar ne bayan ƴan sanda sun gano gawar yarinyar a makarantar.

Da ya ke nuna takaici a kan lamarin a wata sanarwa da ya fitar, Ƙiru ya ce gwamnati za ta fara tantance makarantu mau zaman kan su domin a fito da wadanda basu da rijista domin magance aiyukan ɓatagari.

Ya kuma yi kira ga iyayen daliban makarantar Noble Kids Academy din da su tsaya da kai ya’yan su har sai an kammala bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here