Gwamnatin Kaduna ta rushe otel ɗin da aka so yin dabdalar nuna tsiraici

Gwamnatin jihar Kaduna ta rushe otel ɗin da aka yi niyyar gudanar da dabdalar nuna tsiraici a jihar.
Mai taimaka wa gwamnan jihar Kaduna kan kafofin watsa labarai Abdallah Yunus Abdallah ya tabbatar wa BBC da faruwar rushe otel ɗin, inda ya ce an rushe Asher otel ne bayan bincike ya nuna cewa a wurin aka yi niyyar gudanar da dabdalar nuna tsiraici.

Ya kuma bayyana cewa otel ɗin wanda ke a Unguwar Barnawa, ya rinƙa saɓa dokokin da gwamnnatin jihar ta shimfiɗa na hana yaɗuwar korona, inda ko a kwanakin baya sai da gwamnan ya yi barazana mai ƙarfi ga wuraren da suka yi kunnen ƙashi.
A makon nan ne dai an ƴan sanda a jihar suka damƙe matasan da suka yi niyyar gudanar da wannan dabdalar a jihar, inda a jikin goron gayyatar aka buƙaci mahalarta bikin su je wurin tsirara
