Gwamnatin Jihar Kaduna ta kori malamai 233 sakamakon amfani da shaidar karatu ta bogi a lokacin ɗaukar aiki da jihar ta yi.

Shugaban Hukumar Ilimin Bai-ɗaya, SUBEB Tijjani Abdullahi, shi ne ya baiyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a yau Alhamis a Kaduna.

Abdullahi ya ce an kori malaman ne mayan da a ka bincika makarantun da su ka ce sun yi, in da hakan ya nuna cewa takardun shaidar karatun na su na bogi ne.

Shugaban SUBEB ɗin ya baiyana cewa tun a watan Afrilu ne a ka fara bincike kan takardun sahidar kammala karatun malaman, inda ya ƙara da cewa an yi hakan ne domin tabbatar da cewa sun bada shaidar kammala karatu sahihiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here