Advert
Home Sashen Hausa Gwamnatin Kaduna ta ce an kashe mutum 343 cikin wata uku a...

Gwamnatin Kaduna ta ce an kashe mutum 343 cikin wata uku a jihar

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum 343 sakamakon ayyukan ‘yan fashin daji da sauran tashe-tashen hankali cikin wata uku.

Cikin wani rahoto da ya fitar ranar Laraba, Kwamashinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa ‘yan bindigar da ake zaton ‘yan fashin daji ne sun sace mutum 830 a watannin.

Rahoton ya duba rikice-rikicen da suka faru ne daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga Satumban 2021.

Sai dai rahoton ya nuna cewa adadin waɗanda aka sace a wata ukun ya ƙaru a kan na watannin Afrilu zuwa Yuni, inda aka sace 774 kuma aka kashe 222.

•Na cire ɗana daga makarantar gwamnati saboda ‘yan fashi na ƙoƙarin sace shi – El-Rufai
•’Yan bindiga sun kai hari Makarantar Sojoji ta NDA
•Abin da ya sa El-Rufai ba ya goyon bayan yin sulhu da ƴan bindiga
•A gefe guda kuma, Mista Aruwan ya ce jami’an tsaro sun kashe jumillar ‘yan fashi 69 a wurare daba-daban na jihar tare da tarwatsa sansanoninsu.

Daga cikin waɗanda aka sace ɗin, Mazaɓar Sanatan Kaduna ta Tsakiya ce ke da 732 bayan an ɗqauke su a ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da Igabi da Chikun da Kajuru. Sai Mazaɓar Kudancin Kaduna da ke biye mata da mutum 51 da kuma Arewaci mai 41.

Kazalika, Kudancin Kaduna ne ke da mafi yawan mutanen da suka mutu da mutum 193, Mazaɓar Tsakiya na da 130 da kuma Arewaci da ke da mutum 20.

Haka nan, an sace dabbobin da suka haɗa da shanu da akuyoyi da tunkiyoyi har 1,018 cikin wata ukun, yayin da aka sace 780 a Mazaɓar Kaduna ta Tsakiya.

Kwamashina Aruwan ya ce rikice-rikicen sun jikkata mutum 210 jumilla.

A watan Satumba ne wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya suka ɗauki matakin toshe layukan sadarwa ciki har da Kaduna da zummar daƙile ayyukan ‘yan fashin.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE BUHARI ADMINISTRATION SUPPORTS THE LAGOS STATE RAILWAY PROJECT!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/232549375628254/

Kotu ta rushe shugabacin jam’iyar APC ɓangaren Ministan Ilimi, Adamu Adamu a Bauchi

Babbar kotu a Jihar Bauchi ta rushe shugabacin Babayo Ali Misau na jam'iyar APC a jihar. Rahotanni sun baiyana cewa shi dai Misau yaron Ministan...

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths editorDecember 5, 2021 4:50 Pm Francis Sardauna in Katsina Ahead of the 2023 general election, the...

‘Yan Bindiga Sun Tsananta Kai Hare-hare Akan Hanyar Gusau Zuwa Shinkafi

Daga Dauda Umar Januhu 'Yan Bindiga a jihar Zamfara suna cigaba da kai zafafan hare-hare tare da sace mutane akan babbar hanyar da ta tashi...

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano…

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano Jami'an Ƴan sandan Farin Kaya, DSS sun kama Janar Idris Dambazau, Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin mai Sayan Kaya...