Advert
Home Sashen Hausa Gwamnatin Jihar Neja Zata Dawo Da Dalibanta Dake Karatu A Jami’ar Jos

Gwamnatin Jihar Neja Zata Dawo Da Dalibanta Dake Karatu A Jami’ar Jos

Gwamnatin jihar Neja ta fitar da sanarwar dawo da ɗaliban jihar ta da ke karatu a jami’ar gwamnatin tarayya dake birnin Jos na jihar Filato biyo bayan rashin zaman lafiya a wasu sassan jihar da ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.

Wannan na cikin wata sanarwa da ta fito ɗauke sa hannun Sakatariyar watsa labaran gwamnan jihar Mary Noel-Barje, inda gwamnatin ta ce matakin hakan ya zama dole bisa yanayin tsaro ya tilasta mahukuntan Jami’ar dakatar da jarrabawar kammala karatun zangon karatun shekarar 2019/2020 na jami’ar.

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta umarci Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Ma’aikatar Makarantun Gaba da Sakandare tare da su shirya motoci da jami’an tsaro da za su dawo da ɗaliban tare da tabbatar da ɗaliban sun dawo lafiya.

Gwamnatin jihar ta sake jaddada ƙudurin ta na kare lafiyar mazauna jihar ba tare da la’akari da yankin da suka fito ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: