Gwamnatin Jihar Neja Ta Koro Almajirai 21 Zuwa Katsina

Gwamnatin Jahar Niger ta maido wa Jahar Katsina Almajirai 21

Gwamnatin Jahar Niger ta turo Almajirai 21 (masu barace-barace) zuwa Jahar su ta Asali wato Jahar Katsina, biyo bayan sanya Dokar hana barace-barace akan Titunan Jahar.

Darakta-Janar ta Hukumar Kula da Haƙƙin Yara Hajiya Mariam Kolo ta bayyana haka a Minna, Babban Birnin Jahar Niger, cewa sun gano yaran ne a Minna akan hanyar su ta zuwa Garin Mokwa, wani ɓangare na Jahar.

An dai ɗauke su ne cikin Mota, daga wani Malam Habibi Abdulrazaka, Mazaunin Suleja, shima daga Jahar ta Katsina.

“Kwanaki uku da suka gabata, mun samu kira cewa wata Mota ɗauke da Almajirai an kama ta.

“An kawo Motar a ofishin mu, inda muka gano cewa yaran dukkanin su, ƴan Ƙasa da Shekaru 17 ne.

“Sun kasance Almajirai wanda suka zo Niger domin Karatun Addinin Musulunci.

“Tunda basu cika sharuɗɗan kasance wa, sun haɗa hannu da wata Ƙungiya ta Addini a Jahar, dole ne mu maida su Jahar su ta Asali,” Inji ta.

bazata amince da dukkanin wani nau’i na barace-barace ba, wanda tuni aka tsaida.

“Yaran da suka cika ƙaidojin da aka Shimfiɗa za’a yi maraba dasu, domin koyon Karatun Musulunci dana Alƙur’ani a Jahar.

“Duk wani Malami dayake kawo yara domin su koyi ilmi, to dole sai ya tabbatar cewa an kiyaye haƙƙin yara, musamman ta fuskar ciyar wa da kyakkyawan wurin kwana.

“Gwamnati bazata taɓa amincewa da shigowar mutane a Jahar ba,” Cewar Darakta-Janar.

Mr Sadiq Yamai Sakataren Shirye-shirye a Cibiyar Binciken Ilmin Alƙur’ani ta Najeriya yace abin ayaba ne, na yadda Gwamnatin ke sanin dukkanin Almajiran da aka kawo wa Niger domin su koyi Ilmin Alƙur’ani mai girma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here