Gwamnatin jihar Neja ta dakatar da haƙar zinari

Gwamnatin jihar Neja a arewacin Najeriya ta bayar da umurnin dakatar da aikin hakar ma’adinai a ƙananan hukumomin Paikoro da Shiroro.
Gwamnatin ta sanar da ɗaukar matakin ne a cikin wata sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin jihar Ahmed Ibrahim Matane ya fitar.
Sanarwar ta ce an dakatar da dukkanin ayyukan haƙo ma’adinan ne a ƙananan hukumomin saboda matsaloli na tsaro da kuma muhalli.
Sakataren gwamnatin ya bayyana cewa dole ne gwamnati ta ɗauki mataki kasancewar lalacewar muhalli da rashin tsaro sakamakon ayyukan masu hakar ma’adanai a yankunan ya kai wani mataki na ban tsoro, wanda kuma ke buƙatar matakin gaggawa don magance matsalolin a ƙanana hukumomin da abin ya shafa.
Sanarwar ta yi kira ga ƙungiyar masu haƙo ma’adinai da kuma shugabannin gargajiya na yankin da su ba gwamnati haɗin kai da kuma hukumomin tsaro.