Gwamnatin Jihar Lagos ta karrama ASP Sunday Erhabor bisa Hakurin shi da Juriya yayin Gudanar da Aikinshi….

ASP Sunday Erhabor dai ya karade shafukan sada zumunta ne yayinda aka nunu wani Faifan Bidiyo Inda yake tuhumar wasu Matasa da suka sa’ba ƙa’idar tuki a Lagos din, amma maimakon subada kai sai suka cigaba da nuna rashin Mutunci akan Jami’in shi kuma yayi hakuri da duk cin Mutunchin da sukayi mashi.

Da haka ne wasu A kafar sadarwar zamani suka yi yekuwar tarama ASP Sunday kudi har Naira Dubu Ɗari Biyar saboda wannan rashin hasala nashi duk kuwada yana riƙe da Makami kuma yana iya daukar mataki amma baiyi hakan ba.

Itama Gwamnatin jihar Lagos ta karrama shi saboda halinda ya nuna kuma ma an bada misali dashi cewa sauran Jami’an tsaro suyi koyi da irin halin shi.

Tuni dai Jami’an tsaron suka kame Matasan da sukayi ma ASP Sunday rashin ta ido zakuma.a hakunta su akan laifin da sukayi na sabama dokokin hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here