Gwamnatin Jihar Katsina za ta ci gaba da mara ma al’umma da jami’an tsaro baya domin tabbatar da an ga bayan ta’addanci tare da samun zaman lafiya a wannan jiha.

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana haka a yau yayin da ya amshi bakuncin Maimartaba Sarkin Karaye ta jihar Kano Dr Ibrahim Abubakar II, wanda ya kawo mashi ziyara a fadar Gwamnatin Jiha.

Ya kara da cewa, wajibi ne gwamnatoci, jami’an tsaro da al’ummomi mu hada kai domin tunkarar wannan ta’annati dake neman zukunar da al’umma gaba daya. Kyale wannan matsala taci gaba ruruwa zai karya kashin bayan al’umma da na tattalin arzikin ta, domin noma da kiwo ake neman durkusarwa gaba daya ga kuma asarar rayuka da tafi komai ciwo.

A nashi jawabin, Maimartaba Sarkin na Karaye Dr Ibrahim Abubakar II ya shaida wa Gwamna Masari cewa ya zo Katsina musamman domin ya jajanta wa Gwamnatin Jiha, Masarautar Katsina da kuma al’umma bisa ibtila’in hare haren ta’addanci da suka addabi wasu kananan hukumomi da kuma gobarar da ta lakume dukiyoyin al’umma na Miliyoyin Nairori.

Maimartaba Sarkin na Karaye, ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rayukan su Ya kuma mayar ma wadanda suka yi asara mafiyin abinda suka rasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here