Gwamnatin jihar katsina zataci gaba da Aiwatar da shirye shirye domin Inganta rayuwar ƴaƴa mata- Aminu Bello Masari

Gwamnatin Jihar Katsina za ta ci gaba da aiwatar da shirye shirye tare da daukar duk matakan da suka dace domin tabbatar da an inganta rayuwar ‘ya’ya mata yadda za su rayu cikin walwala da sanin ya kamata.

Gwamna Aminu Bello Masari ya fadi haka yau yayin da ya kaddamar da kundin TSARIN INGANTA RAYUWAR ‘YA’YA MATA A JIHAR KATSINA DAGA SHEKARAR 2020 ZUWA 2023 wanda Ma’aikatar kula da harkokin mata ta jiha ta shirya.

Alhaji Aminu Bello Masari ya kara da cewa lokaci ya yi da zamu farka kuma mu gane cewa ilmantar da mata ba karamin muhimmanci ke gare shi ba wajen ginawa da kuma ci gaban al’umma. Ya kuma yi kira ga iyaye da su guji yaran su tallace tallace domin gujewa gurbacewar tarbiyya da kuma zamewarta tarnaki gare su wajen neman Ilimin Islama da na boko.

A nashi jawabin, Mai ba Gwamna Shawara a kan ilimi mai zurfi Muhammad Bashir Ruwan Godiya yayi fassara ne a takaice tare da yin fashin baki a kan wannan kundi mai dauke da bayanan halin da muke ciki a yanzu da kuma inda ake fatar kaiwa.

Tun farko a nashi jawabin, Shugaban taron, Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi, Mai Shari’a Sadiq Abdullahi Mahuta, kira yayi ga iyaye da suba Ilimin mata muhimmancin gaske domin ceto al’umma daga rushewa, domin kuwa mata sune iyayen al’umma kuma tushen ginin tarbiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here