Advert
Home Sashen Hausa Gwamnatin jihar katsina zata kula da yara daga shekara 15 waɗanda suka...

Gwamnatin jihar katsina zata kula da yara daga shekara 15 waɗanda suka rasa iyayen su sanadiyyar ƴan bindiga a jihar

GWAMNATIN JIHAR KATSINA ZATA KULADA RAYUWAR YARA DAGA SHEKARA (15) DA SUKA RASA IYAYEN SU SANADIYAR RIKICIN YAN BINDIGA BARAYIN SHANU A JIHAR KATSINA.

Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Aminu Bello Masari ya bayyana haka yau Alhamis 05/11/2020 a fadar Gwamnatin Jihar Katsina lokacin daya amshi bakuncin tawagar shugabannin Kungiyar yan sintiri (Vigilant Group) a turance, ta kasa baki daya kalkashin jagorancin shugaban Kungiyar kwamanda Janaral Dr. Usman Muhammad Jahun.

Kwamanda Janaral da tawagar shi sun kawo wannan ziyara ne Jihar Katsina, don karfafa gwiwa ga Kungiyar yan sintiri ta Jihar Katsina kan aikin yaki da yan ta’addar barayin shanu, da masu Garkuwa da mutane don neman kudin fansa da suke aikata ayyukan ta’addancinsu a Jihar Katsina.

Tunda farko a nashi jawabin Shugaban Kungiyar Dr. Usman Jahun ya bayyana ma Maigirma Gwamnan “cewa Kungiyar yan sintiri ta Jihar Katsina tana membobi dubu ashirin da shidda (26,000) , munzo Jihar Katsina don taimaka ma aikin yan sintirin na yaki da yan bindiga da suke aikata ayyukan ta’addanci a Jihar Katsina. Ya kara da “cewa Goyon baya kawai muke bukata, insha Allahu zamu shiga cikin dajin da yan ta’addar suke kuma da taimakon Allah sai an kawo karshen ta’addansu.

Da yake gabatar da jawabin shi , Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari “ya nuna farin cikin shi kan wannan ziyara da Kungiyar yan sintirin ta kawo Jihar Katsina don taimaka ma aikin samar da tsaro a Jihar Katsina. Gwamnati a shirye take ta bada duk gudumuwar data dace kan aikin yan sintirin”

Har ila yau Maigirma Gwamnan ya cigaba da bayyana “cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta shirya komiti na musamman wanda zai binciko tareda kididdiga kan yara daga shekara (15) da suka rasa iyayen su sanadiyar rikicin na yan bindiga a Jihar Katsina, don kulawa da rayuwar su.

Daga karshe Gwamnan “yayi kira ga Kungiyar yan Sintirin dasu tashi tsaye don tsarkake aikin yan sintirin, domin akwai bata gari da suke shigowa cikinku suna bata maku aiki da sunan yan sa kai”. Shugabannin Kungiyar yan sintiri (Vigilant Group) a turance, ta Jihar Katsina kalkashin jagorancin shugaban Kungiyar Alh. Salisu Rabo sukayi rakiya ga shugabannin Kungiyar na kasa zuwa fadar Gwamnatin Jihar Katsina.

Daga cikin yan majalisar zartarwa ta Jihar Katsina da suka halarci taron ziyarar Kungiyar yan sintirin, akwai Kwamishinan ma’aikatar Ilmi ta jihar Katsina Prof. Badamasi Lawal Charanci, kwamishinan ma’aikatar kasa da safiyo Alh. Usman Nadada, Mai baiwa Gwamna Shawara kan Ilmi mai Zurfi Dr. Bashir Usman Ruwan Godiya. Dadai sauransu.

Rahoto.
Surajo Yandaki
Edita, Mobile Media Crew
05, November 2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM’IYYAR APC?….Siyasar zaben 2023

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM'IYYAR APC? . ..Siyasar Zaben 2023 Mu'azu Hassan @ Katsina City News Yanzu saura shekara daya da watanni a yi sabbin zabubbakan...

Bikin bada sandar girma a Masarautar Rano

Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya Jagoranci mika sandar Girma ga Mai Martaba Sarkin Rano, Amb. Alh. Kabiru Muhammad Inuwa Autan...

Majalisar Dinkin Duniya Ta Sake Nada Amina Muhammad Daga Jihar Gomben Najeriya Karo Na Biyu

Majalisar Dinkin Duniya, karkashin shugabancin Antonio Gutterres ta amince da sake nada Amina Muhammad, mataimakiyar sakatare janar na wasu shekaru biyar masu zuwa. An sake...

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021 DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO A YAU, 18 ga Yuni, 2021 Alhaji Dakta Mamman Shata Katsina, MON, ya...
%d bloggers like this: