Advert
Home Sashen Hausa Gwamnatin Jihar Katsina Tayi Allah Wadai Da Haddasa Mutuwar Mutane I0 Da...

Gwamnatin Jihar Katsina Tayi Allah Wadai Da Haddasa Mutuwar Mutane I0 Da Jami’an Hukumar Hana Fasa Kwabri Suka Yi A Jibia.

Gwamna Aminu Bello Masari yayi Allah wadai da tare da nuna bacin rai akan haddasa mutuwar mutane da basu ji ba basu gani ba da Jami’an Kwastam sukayi ta hanyar tukin ganganci a Karamar Hukumar Jibia.

Gwamnan ya bayyana cewar gwamnati ba zata cigaba da lamuntar irin wannan ganganci ba.

Matsayin Gwamna Masari na zuwa ne a dai-dai lokacinda yake tsokaci akan lamarin da ya afku a lokacinda wasu Jami’an Hukumar Hana Fasa Kwabri ta Kasa sukayi sanadiyar macewar mutane I0 a ranar Litinin da ta gabata.

A sa’ilinda Gwamnan yake mika sakon jajantawa ga iyalan wadanda lamarin ya ritsa da su,yayi horon cewa gwamnatinsa ba zata zura ido ana kashe mutane a irin wannan lamari ba wanda jami’an ma kamata yayi su kare rayukan Jama’a.

Yace Gwamnatin Jihar Katsina na duba yiyuwar daukar matakin shari’a akan Hukumar ta Kwastam domin lamarin ya zama darasi nan gaba wanda hakan na faruwa a kowace rana a Jihar.

Signed.
Abdu Labaran Malumfashi,DG Media
I3-08-202I

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: