Gwamnatin Jihar Katsina tana kara godiya da jinjina ga al’umma bisa ga fahimta, goyon baya da kuma gudummawar da suke badawa wajen yaki da ta’addanci da kuma ‘yan ta’adda.

Wannan na kunshe cikin bayanin bayan taron Majalisar zartaswa ta jiha da akayi yau a babban dakin taro na Gidan Janar Muhammadu Buhari, fadar Gwamnatin Jihar.

Ganin yadda al’umma suke nuna fahimta ga matakan da Gwamnati ke dauka na dakile ta’addanci tare kuma da yin hobbasa wajen kare kai, ya zama wajibi ayi masu godiya ta musamman domin a zaburar dasu, domin duk nasarar da aka samu da goyon bayan su aka same ta.

Haka kuma, gwamnati, tana jan hankalin al’umma da suka sa ido sosai wajen gano bata garin cikin mu da suke aike ma ‘yan ta’adda da bayanai (informers) domin hadarin su yafi na masu ta’addancin domin su ke bada bayanan da masu ta’addancin suke amfani dasu suna ma al’umma zilla.

Mai ba Gwamna Shawara a kan harkokin tsaro Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina wanda ya yayi wani jawabi, ya bada tabbacin cewa aikin da aka fara da kananan hukumomin Jibia da Batsari, za aci gaba dashi har sai an tabbatar da an kakkabe ‘yan ta’addar da suka addabi al’umma.

A daya bangaren kuwa, Majalisar zartaswar ta amince da irin kalolin fentin da za ayi wa motoci da kurkurori na haya da ake amfani dasu a fadin jihar nan. Haka kuma za a fitar da alamomi da kuma lambobin da za su banbance su tsakanin kananan hukumomin da suka fito. Kwamishinan Ayyuka da gidaje ya bayyana hakan a yayin wannan zama da akayi da manema labaru, tare da cewa hakan duk yana cikin kokarin tsare lafiya da dukiyoyin al’ummar jihar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here