Kauran Katsina Hakimin Rimi Alhaji Nuhu Abdulkadir

Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara akan harkokin tsaro Alh. Ibrahim Katsina ya bayyana haka ranar Alhamis 24/06/2021 yayin da ya jagoranci wani Kwamitin wuccin gadi zuwa kananan hukumomin Batsari da Danmusa, a cikin aikin Kwamitin ya fara na ziyartar kananan hukumomin Jihar Katsina (34) ya kaddamar da wasu Kwamitoci guda uku.

Alh. Ibrahim Katsina ya cigaba da cewa” Shidai wannan Kwamitin wuccin gadi Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya kafa shi domin ya zagaya kananan hukumomin Jihar Katsina ya kaddamar da kwamitoci kalkashin masu rike da kananan hukumomi da masu rike da masarautun gargajiya domin taimakama aikin samar da tsaro.

“Kafa Kwamitin ya biyo bayan yima dokar kananan hukumomi garambawul da majalisar Dokokin Jihar Katsina tayi, bayan bukatar hakan da Gwamnan ya aikama majalisar, an gyara dokar yadda zata ba masu rike da kananan hukumomi da masu rike da masarautun gargajiya cikakkar damar kula da zamantakewar Al’umma ta kowane bangare domin inganta harkar tsaro”.

Ya kara da cewa” fidda masu rike da masarautun gargajiya daga cikin kula da zamantakewar Al’umma na daya daga cikin abinda ya assasa rashin tsaron da muke fama dashi a halin yanzu, domin anbar Al’umma kara zube kowa na abinda yaga dama ba tare da tsawatawa ba. Da yaddar Allah Munada kyakykyawar fata maido Martabar masu rike da masarautun gargajiya zai taimaka wajen daidaituwar al’amurra zaman lafiyarmu ya dawo kamar da yadda kowa ya sanshi.

Kwamitocin mataki uku ne, Kwamiti mataki na farko shine matakin karamar hukuma wanda shugaban karamar hukuma ke jagoranta, wanda ya hada da Hakimmai, Jami’an tsaro dake kula da harkar tsaro a karamar hukuma, Limamai, da shugabannin Al’umma kowane bangare, Kwamiti Mataki na biyu shine wanda Hakimi zai jagoranta wanda ya hada da Magaddai, Jami’an tsaro, Limamai, da shugabannin Al’umma, yayin da Kwamiti mataki na uku zai kasance kalkashin jagorancin Magaddai wanda ya hada da Masu Unguwanni. Dadai sauransu.

Aikin Kwamitocin kula da zamantakewar Al’umma na shige da ficcensu na yau da kullum, da kuma yin sasanci a tsakanin zamantakewarsu na yau da kullum na wani abu da ya taso, wanda zasu iya sasanci zasu sasanta wanda zasu kai ga Jami’an tsaro zasu kai, Kwamitin zai rika zaman tattaunawa sau daya ko sau biyu a sati don tattara bayanan sirri wadanda suka shafi harkar tsaro, Hakimmai zasu rika bada bayanai ga masarauta, masarauta kuma ta sanar da Gwamnati.

Kwamitin wuccin gadin akwai wakilci daga Gwamnati wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr. Mustapha M. Inuwa yake wakilta, wakilci daga Jami’an tsaro na Yan Sanda, Sojoji, Yan Sandan Farin kaya, dadai sauransu, sai wakilci daga masarautar Katsina da Daura, masarautar Katsina ta samu wakilcin Kauran Katsina Alh. Nuhu Abdulkadir, yayin Masarautar Daura ta samu wakilcin Sardaunan Daura.

A kananan hukumomin Batsari da Danmusa da Kwamitin wuccin gadin ya kaddamar da kwamitocin Hakimman Batsari da Wagini da Hakimman Danmusa da Yantumaki sun bayyana jin dadinsu akan wannan dama da aka maido masu, sun cigaba da cewa” zasuyi iya bakin kokarinsu domin ganin zaman lafiya ya dawo a Jihar nan, tunda an maido da dokar data basu cikakkar damar bincikar zamantakewar Al’umma. Daga karshe sun yabama Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari akan kokari da ya yi na maido da wannan doka data basu cikakkar damar bincikar zamantakewar Al’umma.

Rahoto
Surajo Yandaki
Edita, Mobile Media Crew
25, June 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here