Advert
Home Sashen Hausa Gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar da kwamitin bawa waɗanda Ibtila'in Gobara ya...

Gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar da kwamitin bawa waɗanda Ibtila’in Gobara ya faɗamawa

Gwamnatin Jihar Katsina ta kaddamar da shirin fara bada tallafi ga wadanda ibtila’in gobara ya shafa a babbar kasuwar Katsina, Fatima Baika Central Market Katsina.

A ranar Talata 31/08/2021 aka kaddamar da shirin fara bada tallafin kudi ga wadanda ibtila’in gobara ya shafa a babbar kasuwar Katsina, watau “Fatima Baika Central Market” watanni biyar da suka gabata, domin rage masu radadi.

Kwamitin kula da bada tallafi ga wadanda ibtila’in gobarar ya shafa a babbar kasuwar Katsina da kuma sake gina kasuwar karkashin jagorancin Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Katsina kuma Kwamishinan Shari’ah na Jihar, Hon. Ahmed Usman El-Marzuq ya kaddamar da shirin fara bada tallafin.

Tun daga ranar da ibtila’in ya afku Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Mai girma Gwamnan Jihar Rt. Hon. Aminu Bello Masari ta kafa Kwamiti na musamman domin ya tantance wadanda ibtila’in ya shafa da kuma kiyasin abinda sukayi asara, wanda Kwamishinan ma’aikatar ayyuka, gidaje da sufuri na Jihar Katsina Hon. Tasi’u Dahiru Dandagoro ya jagoranta, bayan gama aikin, Kwamitin ya gano cewa” mutum dari shidda da tamanin da biyar ne (685) ibtila’in gobarar ya shafa, kuma kiyasin asarar da suka tabka yakai naira miliyan dari tara da dubu dari biyar (N900, 500,000).

Bayan Kwamitin ya mika ma Gwamnati Rahoton binciken shi, Gwamnatin Jihar Katsina tayi Alkawalin bada tallafin kashi 40% daga cikin dari na daga cikin abinda ‘yan kasuwar suka rasa, wanda ya kama N361,000,000, daga cikin wannan kaso Gwamnatin ta fara da biyan kashi 68.65% wanda ya kama N247,819,025.92, wanda ya rage kashi 31.35%, wanda ya kama N113,180,974.08.

Sudai wadannan kudade da akaba ‘yan kasuwar tallafi gudumuwa ce daga cikin albashin ma’aikatan jiha dana kananan hukumomi, da kuma albashin masu rike da mukaman siyasa, wanda aka hada N70,708,238.00, yayin da aka samu gudumuwa daga wajen daidaikun Al’umma da Kungiyoyi, wanda aka samu N177,110,000.50

Yayin kaddamar da bada tallafin, shugaban Kwamitin Hon. Ahmed Usman El-Marzuq yaba ‘yan kasuwar hakuri akan jinkiri da aka samu, wannan ya samo asali ne duba da matsalar tattalin arziki data tsaro da kasar nan take ciki wanda ya shafi Jihar Katsina, haka zalika ya yi kira” ga ‘yan kasuwar da dasu roki Allah ya sanya ma abinda suka samu albarka, domin komin yawan abu, idan Allah bai sanya mashi albarka ba, bazai habbaka ba, amma komin kankantar abu, idan Allah ya sanya mashi albarka zaya habbaka, daga karshe yaba ‘yan kasuwar tabbaci bada jimawa ba, Gwamnati zata cigaba da aikin sake gina kasuwar domin Al’umma su dawo su cigaba da gudanar da harkokin kasuwanci kamar yadda suka saba.

Da yake gabatar da jawabin godiya Amadadin yan kasuwar, shugaban Babbar kasuwar ta Katsina watau, “Fatima Baika Central Market” Alh. Abbas Labaran Albaba ya godema” Gwamnatin Jihar Katsina akan wannan kokari da tayi na bada tallafi ga Al’ummar kasuwar Katsina da ibtila’in gobarar ya shafa watannin baya da suka gabata, daga karshe ya yi kira ga Gwamnatin data juyo wajen sake gina kasuwar bayan bada tallafin, domin Al’ummar da wannan abu ya shafa su samu wurin da zasu raba su cigaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu.

Shima da yake gabatar da jawabin shi, daya daga cikin wadanda suka amshi tallafin shugaban matasa na Babbar kasuwar Katsina, watau “Fatima Baika Central Market” Alh. Bello Badaru Alfa ya godema” Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari akan kulawar gaugawa da ya basu akan wannan kaddara data same su, wanda har gashi an basu tallafi don rage masu radadi akan jarabawar da suka shiga, ya cigaba da cewa” an samu gobara a babbar kasuwar Katsina a Gwamnatocin baya, amma basu samu tallafi ba cikin sauri kuma mai tsoka kamar wannan Gwamnati ta Masari. Daga karshe yace” suna tare da Gwamna Aminu Bello Masari, duk inda yace su nufa can zasu nufa.

Tallafin da aka mika masu ta hanyar basu chak, chak na banki, an gudanar da taron a Babban dakin taro na “Katsina Motel”, dake cikin garin Katsina, an kuma raba shirin bada tallafin gida biyar, an fara daga yau Talata 31/08/2021 yayin da za’a kammala zuwa ranar Juma’a 3/09/2021. Sauran yan Kwamitin sun hada da, Alh. Lawal Aliyu Daura Mai baiwa Gwamna Shawara akan bunkasa cigaban Al’umma, Hon. Abubakar Yusuf Saulawa, Mai baiwa Gwamna Shawara akan bunkasa kasuwanni, wakili daga hukumar yan sanda, wakili daga hukumar kare fararen hula, wakili daga hukumar farin kaya, wakili daga Kungiyar Izala da Darika. Dadai sauransu.

 

Rahoto

Surajo Yandaki

Edita, Mobile Media Crew

01 September, 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: