Kwamishinan Matasa da Wasanni Hon. Sani Aliyu Danlami a wajen Jaje garin Barawa

A Ranar Lahadinda ta gabata ne yan bindiga dauke da manyan makamai sukayi dirar mikiya a Kauyen Barawa dake a Karamar Hukumar Batagarawa.

Mutane biyu dai ne yan bindigar suka hallaka a yayin harin tare da jikkata wasu da dama.

A sabili da wannan ne Gwamna Aminu Bello Masari ya tura wata tawwaga a karkashin jagorancin Kwamishinan Wasanni Da Walwalar Jama’a Alhaji Sani Aliyu Danlami domin jajantawa wadanda harin ya shafa a madadin Gwamnatin Jiha.

Haka zalika Gwamnatin ta bayar da gudummuwar kudi naira dubu dari-dari ga iyalan wadanda suka rasu a yayinda wadanda suka samu raunuka aka basu tallafin naira dubu 50,000 kowannensu gami da buhunan shinkafa.

Alhaji Sani Aliyu Danlami yayi addu’a akan Allah SWT yayi rahama ga wadanda suka rasu sakamakon harin.

Yace Gwamna Aminu Masari ya dauki nauyin jinyar wadanda suka samu raunuka a sabili da harin.

Kwamishinan yayi addu’a akan Allah ya kawo karshen matsalolin tsaro dake addabar Jihar Katsina da Kasa baki daya.

Daga garin Barawa Tawagar Kwamishinan ta ziyarci Asibitin Kwararru dake Katsina Domin duba wadanda suka samu raunuka sakamakon harin.

A cikin tawwagar akwai Darakta a Hukumar Bada Agajin Gaugawa ta Jihar Katsina Alhaji Iliyasu Rafukka da Mai Taimakawa Kwamishinan Wasanni na Musamman Alhaji Abdulrazak Yahaya AY da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here