Da Duminsa: Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da jadawalin fara jarabawar tantance daliban da za ta biya ma kudin jarabawar WAEC da NECO

Karanta ka san ranakun da sunayen darussan gaba dayansu

Daga, Ibrahim M Bawa

Gwamnatin jihar Katsina ta sanya ranar Laraba a matsayin ranar da za ta fara gudanar da jarabawar tantance daliban sakandare yan aji shida da za ta biya ma kudaden jarabawar WAEC da NECO idan sun lashe jarabawar.

Kamar yadda Katsina Daily Post News ta gani ma’aikatar ilimin jihar Katsina ce ta fitar da jadawalin fara zana jarabawar ta shekarar 2020 domin tantance daliban.

Ya yadda aka sanya jadawalin fara jarabawar;

Ranar Laraba 7/4/2021 za a yi Lit In English da Book Keeping/Technical Drawing

Ranar Alhamis 8/4/2021 za a yi Mathematics da Islamic Studies/CRS

Ranar Jumu’a 9/4/2021 daliban za su rubuta jarabawar turanci watau English Language.

Ranar Asabar 10/4/2021 za su rubuta jarabawar Civic Education da Metal Work/Wood Work/ Building Construction/ Agriculture

Haka kuma a ranar Litinin 12 ga watan 4 na 2021 daliban sakandaren za su rubuta jarabawar Chemistry/Hausa/Fin Acct sai kuma Commerce/History/Biology

Ranar Talata 13/4/2021 za su rubuta jarabawar Physic/Islamic History sai kuma Geography/Data Processing

Ranar Laraba 14/4/2021 za a rubuta jarabawar Tourism/Animal Husb/Marketing/Catering Craft da Office Practice/Arabic

Sai ranar karshe Alhamis 15/4/2021 za a rubuta jarabawar Social Studies/Govt/Basic Education da kuma jarabawar Economics/Furniture Marking

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here