Ma’aikata nata guna guni…..

Gwamnatin Jihar Katsina ta cire kashi 3% daga cikin albashin ma’aikatan jihar na watan Yuni, a matsayin gudummawar su ga waɗanda lamarin iftila’in Gobara ya rutsa da su a Kasuwar Fatima Ɓaika ko central market Katsina.

Dayawan ma’aikatan jihar da suka amshi albashin watan Yuni, sun bayyana cewa sun ankare da giɓin da suka samu cikin Albashin nasu.

Idan dai ba’a manta ba gwamnatin jihar Katsina ta sanar da cewa dukkan ɓangarorin ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa, za su bayar da gudummawar wani ɓangare na albashinsu don tallafawa waɗanda iftila’in gobara ya shafa a babbar kasuwar ta Katsina.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa “za a cire kaso uku daga albashin dukkan Ma’aikatan Gwamnati daga matakin Aiki na Ɗaya 01 zuwa na Goma Sha Hudu 14 yayin da za a cire kashi Ashirin 20 cikin Ɗari 100 daga Albashin Gwamna da na mambobin majalisar zartarwa Amma ragowar zai kasance na wata ɗaya ne kaɗai”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here